Blatter ya bayyana hakan ne a birnin Zurich na Switzerland a ranar Litinin, bayan da kwamitin ladaftarwar hukumar ta FIFA ya bayyana hukuncin a kan sa.
Kwamitin dai ya haramtawa Blatter da kuma Michel Platini, wanda a baya ke rike da mukamin mataimakin shugaban FIFAr shiga duk wata harkar da ta shafi shugabanci, ko jagorantar kwallon kafa a dukkanin matakai.
Sai dai yayin da yake maida martani kan wannan hukunci, Blatter mai shekaru 79 da haihuwa, ya musanta zargin karya doka, wajen biyan kudi kusan dalar Amurka miliyan 2 daga asusun FIFA zuwa Platini a watan Fabarairun shekarar 2011, yana mai cewa ya gudanar da hakan ne bisa amincewa da yarjejeniyar da aka cimma, bayan gasar cin kofin duniya ta shekarar 1998 wanda FIFA ta gudanar. Inda karkashin wannan yarjejeniya aka yarjewa Blatter ya yiwa FIFA aiki sa'an nan a biya shi daga baya.
Sai dai a daya bangaren kwamitin binciken da FIFA ta kafa ya musanta wannan yarjejeniya. Kwamitin ya ce matakan da Blatter ya dauka ya sabawa dukkanin dokokin hukumar.