Yayin wasan na ranar Lahadi De Graafschap ce ta fara jefa kwallon a zaren Ajax ta hannun dan wasan ta Arek Milik, kafin kuma Ajax din su farke wannan kwallo ta hannun Kristopher Vida. Sai kuma kwallon Riechedly Bazoer wadda ya jefa a zare cikin minti na 70 ana daf da tashi daga wasan.
A dai ranar ta Lahadi Feyenoord ta sha kashi hannun NEC da ci 3 da 1, a wasan su na karshe na kakar bana. Sai kuma PSV wadda ta doke PEC Zwolle da ci 3 da 2. Kana Vitesse ta lallasa FC Twente da ci 5 da1, yayin da kuma Heracles Almelo ta doke FC Groningen da ci 2 da 1.
Yanzu haka dai Ajax ta kammala wasannin rabin kakar bana da maki 41 a wasanni 17 da ta buga, inda take biye da mai rike da kambin kasar wato PSV mai maki 38. Sauran kungiyoyin dake saman teburin sun hada da Feyenoord mai maki 36, da Heracles Almelo mai maki 30 da kuma Vitesse mai maki 28.