Kafin kammala wasan da Liang ya buga da David Grace, sai da 'yan wasan biyu suka shafe sa'oi 5 suna dauki ba dadi gaban 'yan kallo. Yanzu haka kuma Liang wanda ke matsayi na 29 a duniya ya samu dama ta biyu a tarihin wasannin sa, inda ya sake zuwa wasan karshe, bayan da a shekarar 2009 ya samu irin wannan dama a birnin Shanghai, amma a wancan lokaci Ronnie O'Sullivan dan kasar Birtaniya ya lashe gasar ta duniya ajin kwararru.
Tuni dai Liang ya samu gurbin shiga gasar da 'yan wasan 16 mafiya kwarewa za su buga a fadar Alexandra dake birnin Landan cikin watan Janairu mai zuwa.
A sauran wasannin da aka buga kuwa, Robertson wanda shi ne zakaran gasar Snooker na shekarar 2013, ya lallasa mai rike da matsayi na daya a duniya wato Mark Selby da ci 6 da nema a wasan daf da na karshe.(Saminu Alhassan)