An yi taron dandalin tattaunawa na bunkasuwar zirga-zirgar sararin samaniya na kasa da kasa karo na 3 a jiya Talata a nan birnin Beijing, inda aka bada labarin cewa, ya zuwa watan Disambar wannan shekara ta 2015, kasar Sin ta kammala harbar tauraron dan Adam na kasuwanci karo 42, inda yawan tauraron dan Adam da ta harba ya kai 48.
A sakamakon bunkasuwar harkokin zirga-zirgar samarin samaniya ta kasar Sin, an samu sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya a wannan fanni. Ya zuwa watan Disamba na wannan shekara, kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da kasashen Rasha, da Brazil, da Pakistan, da Venezuela da kuma sauran kasashe da hukumomi fiye da 30, don raya harkokin zirga-zirgar sararin samaniya. (Lami)