Hukumar samar da abinci ta duniya FAO ta yi gargadi dangane da illar da karuwar dumamar yanayi wato El Nino za ta iya haifarwa a kan amfanin gona da kiwon dabbobi a yankunan kudancin Afrika.
Mai magana da yawun MDD ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talatar nan.
A wani gargadi na musamman da cibiyar samar da bayanai da ba da gargadin gaggawa ta duniya GIEWS ta hukumar FAO, ya nuna cewar, tuni kasar Afrika ta kudu ta kaddamar da shirin yaki da fari a wasu lardunan kasar biyar, musamman yankunan da suka fi noma amfanin gona nau'in alkama, yayin da a Lesotho aka tsara wani jadawali na tunkarar matsalar ta fari, sai kuma a kasar Swaziland inda aka kaddamar da shirin adana ruwa bayan la'akari da yadda ma'ajiyar ruwan kasar ta yi kasa sosai.
A cewar FAO, El Nino, wani nau'in sauyin yanayi ne wanda galibi yana faruwa ne a sakamakon dumamar tekuna a yankunan tsakiya da gabashin tekun Pacific. Ya kan faru ne bayan shekaru 2 zuwa 7, sannan ya kan dauki tsawon watanni 18. Kuma a lokacin faruwar wannan al'amari, yanayi ya kan canza, kuma yana haddasa mumunan sauyin yanayi wanda ke shafar duniya baki daya.(Ahmad Fagam)