in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara miliyan 1 sun bar makarantu dalilin rikicin Boko Haram, in ji UNICEF
2015-12-23 10:18:37 cri

Tashe tashen hankali kan fararen hula a arewa maso gabashin Najeriya da kuma kasashe makwabta sun tilastawa yara miliyan guda barin makaranta, in ji asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) a ranar Talata.

A kasashen Najeriya, Kamaru, Chadi da Nijar, fiye da makarantu dubu biyu ne aka rufe dalilin rikicin Boko Haram, kana an kai wa wasu daruruwan makarantun hari, an lalata su ko sanya masu wuta, in ji UNICEF a cikin wata sanarwa.

UNICEF ya bayyana cewa, adadin yaran da aka dakatar da karatunsu dalilin rikicin Boko Haram ya karu tare da wasu yaran miliyan goma sha daya da shekarunsu suka kai shiga makarantar firamare da tuni kuma aka fidda daga makaranta a cikin wadannan kasashe hudu tun ma kafin barkewar rikicin.

Adadi ne mai tada hankali sosai, in ji Manuel Fontaine, darektan UNICEF a shiyyar yammacin Afrika da ta tsakiya.

Wannan rikici wata babbar matsala ce ga ilimi a shiyyar, kuma tashin hankali na nisantar da yawancin yara daga dakunan daukar darasi tun fiye da shekara guda, halin da ka iya tilasta musu barin karatu baki daya, in ji jami'in.

Har ila yau, kimanin malaman makaranta 600 aka kashe a Najeriya tun farkon barkewar tawayen Boko Haram.

UNICEF ya jaddada cewa, ya taimaka wajen sake shigar da yara dubu 170 makaranta a yankunan da suka fi samun tsaro na jahohin Najeriya uku da rikicin ya fi kamari, inda aka sake bude yawancin makarantun.

A halin yanzu, babban kalubale shi ne na tabbatar da tsaron yara ba tare da dakatar da karatunsu ba, in ji mista Fontaine. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China