in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana ra'ayinta kan shigowar jirgin sama mai jefa boma-bomai da Amurka ta yi ba tare da samun izni ba
2015-12-19 14:06:00 cri

Ofishin yada labaru na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya ba da labari a yau Asabar 19 ga wata cewa, Sin za ta dauki duk matakin da ya dace don kiyaye ikon mulki da tsaron kasar.

Yayin da manema labaru suka gabatar da tambaya game da wani jirgin sama mai jefa boma-bomai na B-52 na kasar Amurka wanda ya shiga sararin tekun kasar Sin a wasu tsibirorin Nansha a makon jiya, ofishin ya sanar da cewa, Sin tana sa ido sosai kuma ta baiwa jirgin gargadin janye jikinsa daga sararin saman kasarta, a cewar ofishin, Amurka ta kan tura jiragen ruwan yaki zuwa sararin tekun kasar Sin don nuna karfinta na makamai, abin da ya kawo babbar barazana ga tsaron ma'aikata da na'urori dake tsibirorin. Matakin da Amurka ke dauka tamkar takala ne, abin da zai tsanantar da halin da yankin Nanhai ke ciki, har ma zai haifar da matsalar soja. Hakan ya sa, Sin da kakkausar murya, tana neman Amurka da ta dauki matakin da ya dace don karaucewar aukuwar kalubaloli da rikicin irin wannan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China