Sin: Yawan wadanda aka hukunta karkashin yaki da barnata dukiyar kasa ya kai fiye da 6,500 a watan Nuwanba
Hukumar nan dake yaki da laifuka masu alaka da cin amanar kasa, karkashin jam'iyyar Kwaminis mai mulkin kasar Sin, ta ce a watan Nuwambar bana kadai, yawan jami'an hukuma da aka hukunta sun kai fiye da mutum 6,500, wanda hakan ke nuna cewa bisa jimilla, a ban kadai an hukunta jami'ai 43,200 a bana.
Cikin wadanda aka ladaftar a cewar hukumar ta CCDI, hadda wasu manyan jami'an larduna, da wadanda suka kai mukamin ministoci su 4. Sa'an nan jami'an da suka fuskanci fushin hukumar, aka same su da hannu cikin wasu laifuka 4,800, wadanda suka shafi zarce iyaka wajen amfani da kudin hukuma, da biyan alawus da ya wuce gona-da-iri, kamar dai yadda hukumar ta CCDI ta bayyana a kan shafin ta na yanar gizo.