Shugabar babban kwamitin tarayyar AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana bacin rai da kaduwa kan kisan mista Brahmi, wanda aka kashe da bindiga a ranar 25 ga watan Yuli bayan ya fito daga gidansa dake cikin wata unguwar yankin Ariana.
Madam Zuma ta yi allawadai da wannan dayen aiki, kuma ta bayyana amincewarta cewa hukumomin kasar Tunisia za su duk wani kokarin da ya kamata domin gurfanar da mutanen da suka aikata wannan kisa gaban kotu in ji sanarwar kwamitin tarayyar AU. Hakazalika jami'ar ta bayyana fatanta na ganin an tabbatar yanayi na gafartawa juna da samun jituwa ta yadda za'a iyar aza harsashi mai kyau ta yadda za'a kawo karshen mulkin wucin gadi a kasar Tunisia domin gina wata kasar Tunisia mai wadata da zaman jituwa. (Maman Ada)