in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzania ta samu shiga zagayen karshe na gasar Cecafa ta bana
2015-11-25 15:36:03 cri
A ranar Talata ne kungiyar kwallon kafar kasar Tanzania, ta zamo ta farko cikin kungiyoyin da suka samu gurbi, a zagayen karshe na gasar kwallon kafar kasashen gabashi da tsakiyar Afirka ko Cecafa, wadda ake bugawa a kasar Habasha.

'Yan wasan karkashin jagorancin koci Charles Boniface sun doke kasar Rwanda da ci 2 da 1 ne a wasan rukunin A, wanda suka buga a filin wasa na Hawassa. Yanzu haka dai Tanzania ta zamo daya daga kungiyoyi 8 da za su buga zagayen karshe na wannan gasa. A ranar Juma'a mai zuwa ne kuma kungiyar kasar Rwanda za ta kece raini da takwarar ta ta kasar Somalia, a wani mataki na samun gurbin buga wasannin gaba, yayin da kuma Tanzania za ta kara da Habasha a ranar Asabar.

A ci gaba da buga wasannin gasar ta Cecafa, Uganda ta lallasa Zanzibar da ci 4 da nema, a wasan rukunin B da suka buga ranar Talata.

Ita kuwa Kenya wadda ke rike da kambin gasar, kashi ta sha a hannun kasar Uganda da ci 2 da nema, a wasan da suka buga a ranar Lahadi.

Yanzu haka dai Uganda ce ke saman teburin rukunin B, za kuma su kara da Burundi a wasan su na karshe a rukunin ranar Asabar mai zuwa. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China