in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pato: Ina son kasancewa a kulun din Firimiya na Ingila
2015-12-16 15:29:58 cri
Fitaccen dan wasan kwallon kafan nan Alexandre Pato, ya nuna sha'awar sa ta shiga daya daga kulub din dake buga gasar Firimiya a watan Janairu, domin ci gaba da kare matsayin da ya samu na fitaccen dan wasan gaba na duniya.

Pato, mai shekaru 26 da haihuwa, ya ce yana sha'awar shiga kulub din dake nahiyar turai ne bayan da a wannan watan ya kammala wasa wa'adin aron tsahon shekaru biyu a kulub din Sao Paulo na Brazil.

Bisa kantiraginsa, zai kasance da kulaf din Corinthians ya zuwa karshen shekarar 2016, to sai dai a nasa bangare, dan wasan y ace za shi da niyar ci gaba da bin tsarin kungiyar.

Tsohon dan wasan kulub din AC Milan, wanda ake ganin Barcelona na zawarcinsa, da ma yiwuwar komawarsa zuwa Italy, ya ce yafi son kasancewa a Ingila.

A hirar sa da jaridar Sunday Telegraph Pato, ya ce kafin ya fara buga wasa a kulub din Milan na kasar Itali a shekarar 2007, ya ga sunan sa ana dangatashi da wasu kulub-kulub na Birtaniya.

Ya ce, an fada masa cewar, kulub din Chelsea yana muradina sa, amma mafarkin sa shine ya buga wasa da kulub din kasar Brazilian tare da Ronaldo. Amma yayin da kulub Milan ya bukace shi, ta hannun Manajan sa, sai ya amince, domin hakan zai bashi damar wasa tare da Ronaldo da Paolo Maldini.

Ya ce, ya san wata rana zan yi sha'awar zuwa Ingila, saboda kuluflika Firimiya su ne na farko a duniya, ana matukar gasar shigar su, kuma yana so ya ganshi a kulub din Ingila. Musamman idan ka kalli yadda suka taka leda da yadda aka tsara filayen wasa da kuma irin sha'awar 'yan kallonsa.

Daga cikin kuluflika Firimiya na Ingila dake sha'awar kulla kwantiragi da dan wasan dai akwai Manchester United, da Liverpool da kuma Chelsea. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China