in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da jadawalin ci gaba da gasar zakarun Turai
2015-12-16 15:31:14 cri
Kulaflikan kasar Sifaniya 3 da suka rage a gasar cin kofin zakarun Turai sun samu abokan karawa, bayan fidda jadawalin kungiyoyi 16 da za su buga sauran gasar.

Atletico Madrid za ta kara da PSV, a wasan da ake kallo a matsayin mai matukar wuya ga sassan biyu, yayin da Real Madrid kuma za ta kara da Roma, kana FC Barcelona za ta kwashi 'yan kallo da Arsenal.

Game da wasan su na gaba, daraktan hulda da 'yan jaridu na kulaf din Real Madrid Emilio Butragueno, ya ce ya zama wajibi su zage damtse, duk kuwa da sa'ar da suka yi na tsallakawa wannan zagaye tare da 'yan wasan su dake cike da koshin lafiya.

Butragueno, ya ce za su kara da kungiya mai karfi, wadda ta taka rawar gani. Ya ce idan kungiyar sa ta yi sakaci ko zaton samun nasara cikin sauki za su gamu da cikas.

A daya hannun kuma Daraktan kungiyar Barcelona Roberto, ya ce sun yi sa'ar kaucewa haduwa da PSG a wannan gaba, amma duk da haka ya amince da kwarewar kungiyar Arsenal wadda da ita ne za su kara a wasan dake tafe.

Shi kuwa a nasa bangare, daraktan kungiyar Atletico Madrid Clemente Villaverde bayyana PSV ya yi a matsayin kungiya mai matukar karfi, wadda a baya ta kafa tarihi mai yawa a nahiyar turai, kungiyar da kuma a cewar sa ko shakka babu za su kai ruwa rana da su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China