in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Messi ya yaba kwazon Neymar
2015-12-16 15:34:00 cri
Dan wasan Barceolna Lionel Messi, ya yaba da irin kwazon da takwaran sa Neymar na kulub din Barcelona ke nunawa tun a shekara ta 2011, a yayin da 'yan wasan ke kalubalantar juna a wasan zagayen karshe na gasar kwallon kafa ta duniya a kasar Japan.

'Yan wasan biyu, sun koma kasar su a wannan makon, domin halartar wasan da ake gudanarwa a kasar a halin yanzu, na shekara shekra.

Messi, ya shedawa hukumar FIFA cewar, a lokuta da dama da suka gabata, tun a wancan lokutan ya lura da irin ci gaban da dan wasan ya ke samu a matsayin sa na dan wasa da kuma a matsayin sa na mutum.

Shi dai Messi, ya taimakawa kulub din Barcelona inda ta lallasa Santos da ci 4-0 a shekarar 2011 a wasan karshe, a lokacin Neymar na da shekaru 19 ne, kuma tun a wancan lokacin ya fara nuna bajintar sa a yayin wasan.

Tun a wancan lokaci ya kasance shahararran dan wasa, kuma a yanzu har ma ya zarce a wancan lokacin, ya kara da cewar abin alfahari ne kasancewar sa a tare da su.

Ana saran Messi, zai fara buga wasa da Luis Enrique's a tsakanin su da China's Guangzhou Evergrande a ranar Alhamis a wasan kusa dana karshe.

Neymar, yana samun sauki daga raunin daya samu a kafar sa, kuma ba'a saran za'a ganshi, sai ranar Lahadi a wasan karshe.

Wanda duk yayi nasara a tsakanin Barcelona da Guangzhou Evergrande shine zai kara da River Plate ko kuma Sanfrecce Hiroshima.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China