A zantawar ta sa da jaridar O Globo, Alves ya ce Neymar dan wasa ne da ya fi Ronaldo wuyar rikewa ga 'yan baya. Kaza lika ya fi sauran 'yan wasa iya sarrafa kwallo, da sauri cikin kuma kwarewa.
A ganin Alves Ronaldo ya na da tasiri wajen cin kwallaye da yawa, da kuma sanya kwallo a zare da ka, amma ba shi da gwanintar rike kwallo da sarrafata tsakanin 'yan wasa kamar Neymar.
A halin da ake ciki dai Neymar zai yi takarar karbar lambar bajimta ta Ballon d'Or, shi da Ronaldo da kuma Messi, a yayin bikin mika lambar da za a yi cikin wata mai zuwa.
Koda yake Alves bai tabbatar da hasashen cewa Neymar zai lashe lambar ta wannan karo ba, duk da haka ya ce akwai yiwuwar dan wasan mai shekaru 23 da haihuwa zai cimma wannan nasara a nan gaba.
Ya ce idan har Neymar na da burin lashe wannan lamba ko shakka ba bu zai cimma wannan bukata, idan yana son zama dana wasa mafi cin kwallaye a Brazil zai iya cimma hakan, duba da irin sha'awar da yake nunawa ga sana'ar sa ta kwallon kafa.(Saminu Alhassan)