Barcelona ta lallasa Real Madrid ne dai da ci 4 da nema, inda 'yan kallo kusan 80,000 suka rika daga wasu kyallaye na nuna rashin gamsuwa da takun shugaban kungiyar. A daya hannun kuma wata kididdiga ta nuna cewa magoya bayan kungiyar ta Real Madrid, sun fi dora alhakin abin kunyar da ya faru ga kungiyar kan shugabanta, maimakon koci ko 'yan wasan kungiyar.
Sai dai maimakon maida hankali kan irin kallon da magoya bayan kungiyar ke masa, Perez wanda ya zanta da manema labaru kwanaki biyu bayan wancan wasa, ya maida hankali ga tsokaci kan kwarewar sabon kocin na Madrid, wanda aka dakko bayan sallamar Carlo Ancelotti a watan Yunin da ya shude.
Perez ya ce koci Rafael Benitez ya cancanci yabo da goyon bayan masoya kungiyar, domin an zabo shi ne bisa kwarewar sa, da kuma gogewa a fagen horas da 'yan wasa. Perez ya kara da cewa yanzu lokaci ne na ci gaba da zage damtse ba wai korafi ba.
Ya ce "Rafael Benitez zai ci gaba da aiki tare da mu…..yana da kwarewa a kan aikin sa…ya samar mana da damar shiga zagaye na gaba na gasar cin kofin zakarun turai da na Sifaniya, kuma mun taka rawar gani, in banda a wasanni biyun karshen nan, duk kuwa da tarin 'yan wasa da muke da su da ke fama da jinya".
Shugaban kungiyar ta Real Madrid ya bukaci goyon bayan da hadin kan masoya kungiyar, wajen cimma karin nasarori ga kungiyar da kuma 'yan wasan ta, yana mai fatan za su samu cikakkiyar damar ci gaba da nuna kwarewar su yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)