in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern Munich ta lallasa Paulaner da ci 6-1
2015-11-10 15:09:17 cri
Bayern Munich ta yi nasara a kan Paulaner Dream Team da ci 6-1 gasar wacce sama da 'yan kallo dubu 12,200 suka halarta a filin wasa na Continental Arena a Litinin din nan.

Tawagar 'yan wasan na kulub din mai horas da 'yan wasa Josep Guardiola's basu nuna sassauci ba ga takwarar su mai dauke da 'yan wasa 30 da suka hada da na kasashen Sin da Turai da kuma Amurka ba.

A karon farko sai dai tawagar ta Munich ta zara kwallaye 4 tun kafin tafiya hutun rabin lokaci. Yayin da Paulaner Dream Team, ta samu damar zara kwallo guda a wani bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda dan wasa Peter Maier ya haddasa.

Bayern Munich ta ci gaba da tsaron gidanta domin kaucewa farmaki daga Paulaner's Dream Team.

Bayan jerin hare haren da Bayern suka sha kaddamarwa, sun kafa tarihi a wasan ne yayin da ya rage mintuna 16 da kammala wasan.

Dan wasan Marcel Reimann yayi nasarar zara kwallo ta 5 ne ga Bayern yayin fara wasan da mintuna 56th.

Bayern ta samu damar kara adadin kwallayenta ne yayin da ya rage mintuna 3 da kammala wasan inda aka tashi da ci 6 da 1. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China