'Yan kwallon Super Eagles din za su fara atisayen ne kafin wasan su na farko, cikin zango na biyu na wasannin fidda gwani wanda za su buga da kasar Swaziland a birnin Lobamba.
A cewar mai magana da yawun kungiyar Toyin Ibitoye, za a fara tara 'yan wasan ne domin samun horo tun da wuri, duba da yadda wasun su ke makara a duk lokacin da ake bukatar su halarci wasa ga kungiyar ta Super Eagles.
Ibitoye ya ce masu tsaron gida ne kadai suka gudanar da atisaye a jiya Litinin, kuma ya zuwa karfe 4 na yammacin jiyan, duka-duka 'yan wasa 8 ne suka halarci sansanin da aka bude ga 'yan wasan. (Saminu Alhassan)