Najeriya ta doke kasar Mali da ci 2 da nema a wasan karshe da sassan biyu suka buga, a filin wasa na Sausalito dake birnin Vina del Mar, matakin da ya baiwa kungiyar damar daukar wannan kofi a karo na 5.
Buhari ya ce kare kambin gasar da kungiyar ta Golden Eaglets ta yi bayan ta dauki kofin a shekarar 2013, wani abun alfahari ne ga Najeriya. Ya ce 'yan wasan sun nuna kwazo, juriya da aiki tukuru, sun kuma nuna kishin kasa wajen tabbatar da wannan nasara a fagen tamaula.
Bugu da kari shugaban Najeriyar ya ce nasarar da Golden Eaglets ta samu ya nunawa duniya ikon Najeriya na taka muhimmiyar rawa a fagen gasannin kasa da kasa.
Baya ga kofin na U-17 wanda hukumar FIFA ke shiryawa, 'yan wasan na Najeriya sun kuma samu nasarar karbar wasu muhimman kyautuka na bajimta, ciki hadda lambar girma ta dan wasa mafi kwarewa, wadda aka baiwa kyaftin din kungiyar Kelechi Nwakali, da na dan wasa mafi cin kwallaye wanda aka baiwa Victor Osimhen.(Saminu Alhassan)