in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada kara yin hadin gwiwa da taimakawa juna tsakanin kasashen kungiyar SCO
2015-07-11 13:22:30 cri

A jiya Jumma'a, an kaddamar da taron koli na kwamitin shugabannin kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai, SCO a birnin Ufa na kasar Rasha. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Vladimir Putin na Rasha da shugabannin kasashen Khazakstan, Khirgistan da Tajikstan da Uzebikstan sun halarci taron.

A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, ya kamata a hanzarta daukar matakan a zo a gani domin kokarin neman ci gaba tare a yankin, da kare kwanciyar hankali da tsaron kasashen kungiyar cikin hadin gwiwa, da kuma kara yin hadin gwiwa a sabbin fanonni, ta yadda za a iya karfafa zumuncin gargajiya da ya dade yana kasancewa a yankin.

Haka kuma, Mr. Xi Jinping ya gabatar da ra'ayoyi 5 kan yadda za a iya bunkasa kungiyar SCO, wato da farko dai, a tsaya kan matsayin bin "ruhun Shanghai" domin kokarin neman ci gaba tare a yankin. Na biyu, a karfafa karfin daukar matakan kafa tushen tsaron yankin. Na uku shi ne, kara yin hadin gwiwa da kuma kara neman sabbin abubuwa na yin hadin gwiwa. Na hudu, kara yin musaye-musaye tsakanin al'ummomin yankin. Na biyar shi ne, ci gaba da bude kofa da koyon juna domin neman bunkasuwar kungiyar SCO.

Bugu da kari, dukkan shugabannin da suka halarci taron, sun yarda da cewa, ya kamata kasashen kungiyar SCO su kara yin hadin gwiwa wajen yakar ta'addanci, da masu tsattsauran ra'ayoyi da wadanda suke son balle kasa. Sannan ya kamata a kara karfin hukumar kula da aikin yakar ta'addanci ta kungiyar SCO, ta yadda za a iya tinkarar kalubaloli da barazanar gargajiya da ba na gargajiya ba domin tsaron yankin. Dadin daddawa dukkansu sun goyi bayan shawarar bunkasa "zirin tattalin arziki na siliki" da kasar Sin ta gabatar. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China