in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci taron koli na kungiyar SCO
2015-07-06 14:31:04 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron ganawa ta 7, na shugabannin kasashe kungiyar BRICS, tare da taro na 15 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai wato SCO, tarukan da za su gudana birnin Ufa na kasar Rasha.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ce ta bayyana hakan, yayin wani taron manema labaru da ya gudana a Litinin din nan a birnin Beijing, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Cheng Guoping, ya yi karin haske game da ziyarar ta shugaba Xi.

Game da taro na 15 na majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar SCO, Cheng Guoping ya ce yayin taron za a tabbatar da tsare-tsaren bunkasa kungiyar ta SCO a sabon yanayin da ake ciki, da shirin hadin gwiwa a fannoni daban daban, da sa kaimi ga kungiyar SCO wajen samun bunkasuwa yadda ya kamata, da kuma taimakawa kasashe mambobin kungiyar wajen tinkarar kalubale, da kuma samun bunkasuwar tattalin arziki.

Haka zalika kuma, Cheng Guoping ya bayyana cewa, a yayin da yake halartar taron a birnin Ufa, shugaba Xi Jinping zai gana da shugabannin kasar Rasha da ma na sauran kasashe. Wannan ne dai karo na biyu da shugaba Xi zai gana da shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin a bana, ana kuma sa ran shugabannin biyu za su kara sa kaimi ga gina zirin tattalin arziki na hanyar Siliki, da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya, da kuma hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa tushen daidaito da suka cimma a yayin ganawarsu a birnin Moscow.

A daya hannun kasashen biyu za su zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin su karkashin inuwar kungiyar BRICS, da kuma kungiyar SCO, za kuma su bunkasa hadin gwiwa game da harkokin kasa da kasa da kuma yankuna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China