in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kokarin tabbatar da cewar cigaban yanar gizo ya amfana ma kowa
2015-12-16 13:55:43 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar laraban nan ya ce kasar tana son kokarin ganin yanar gizo na intanet ba kawai ya amfana ma Sinawa ba har ma da sauran al'ummar duniya baki daya.

Mr. Xi ya fadi hakan ne a jawabin da ya gabatar wajen bikin kaddamar da babban taron yanar gizo na biyo a duniya da aka bude a birnin Wuzhen dake lardin Zhejiang a gabashin kasar Sin.

Ya ce Sin tana shirin kaddamar da cigaban fasahar yanar gizon da dabarun manyan kafofin adana bayanai da kuma shiri mai lakabin Internet plus a nan da shekaru 5.

A yanzu da ake nazarin samar da tabbaci da kuma kyautata al'adun yanar gizon, Shugaba Xi ya ce kasar za ta tabbatar da cigaban tattalin arzikin wannan bangare, ta kuma habaka huldar kafar da tattalin arziki da cigaban walwalan jama'a.

Shugaban ya ce kasar Sin ta dora babban muhimmanci a kan maganar cigaban fasahar yanar gizo na internet.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China