in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da firaministan Rasha
2015-12-15 21:39:20 cri
A yau Talata 15 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan Rasha Medvedev a garin Wuzhen na lardin Zhejiang na Sin.

A yayin ganawar ta su, Shugaba Xi ya bayyana cewa, an cimma matsaya daya tsakanin sa da shugaban kasar Rasha mista Putin, game da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a duk fannoni tsakanin kasashen Sin da Rasha. Kuma ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen biyu su kara kokari wajen nazari game da sabuwar hanyar yin hadin gwiwa tsakaninsu.

A nasa bangare, mista Medvedev ya bayyana cewa, Rasha na fatan kara yin mu'amala da hadin gwiwa da Sin kan harkokin duniya, da karfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban bisa tsarin SCO da na AIIB.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China