in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karo na farko yawan jarin da kasar Sin ta zuba a ketare a shekarar 2013 ya wuce dalar Amurka biliyan 100
2014-09-09 17:29:05 cri

Ranar 9 ga wata, a yayin taron baje kolin zuba jari na kasa da kasa karo na 18, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da hukumar harkokin kididdiga ta kasar Sin da hukumar kula da kudaden musaya ta kasar Sin sun gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa dangane da yadda kasar Sin ta zuba jari kai tsaye a ketare a shekarar 2013.

Sanarwa ta nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da yawan jarin da kasar Sin ta zuba a ketare a shekarar 2013 ya wuce dalar Amurka biliyan 100, inda ya kai dalar Amurka biliyan 1078.84, wanda ya karya matsayin bajinta a tarihi.

Amma Fang Wei, mataimakin shugaban sashen zuba jari a ketare da yin hadin gwiwa da kasashen waje na ma'aikatar kasuwancin kasar ya ce, kasar Sin ba ta zuba jari a ketare kai tsaye da wuri ba, amma ta samu saurin bunkasuwa, amma yawan jarin da ta zuba a ketare bai fi na kasashe masu sukuni yawa ba, wanda ya kai kashi 10.4 cikin dari kawai makamancin lokacin da kasar Amurka ta zuba, kana kashi 35 cikin dari makamancin lokacin da kasar Birtaniya ta zuba.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China