in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba wa kasashen waje a watanni 3 na farkon wannan shekara ya karu
2015-04-16 15:46:12 cri

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Shen Danyang ya bayyana a yau Alhamis cewa, yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba wa kasashen waje a watanni 3 na farkon wannan shekara ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 158.09, wanda ya karu da kashi 29.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta yi, an ce, yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen waje a watan Maris na wannan shekara ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 51.43, wanda ya karu da kashi 0.4 cikin dari bisa na makamancin lokaci. A watanni 3 na farkon wannan shekara, kasar Sin ta zuba jari kai tsaye ga kamfannoni 2331 na kasashe da yankuna 142.

A gun taron manema labaru, Mr. Shen Danyang ya ce, a wadannan watanni 3, yawan jarin da babban yankin kasar Sin ya zuba wa muhimman yankuna da kasashe 7 mafi cigaban tattalin arziki ciki har da yankin Hongkong na kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya da kungiyar EU da kasashen Australia da Amurka da Rasha da kuma Japan ya dauki kashi 77.5 cikin dari bisa na daukacin yawan jarin da kasar ta zuba wa kasashen waje.

Haka zalika, Mr. Shen ya kara da cewa, ban da kididdigar da bankuna da kasuwannin cinikin takardun hada-hadar kudi da kuma kamfanonin inshora suka bayar, yawan kudin kasashen waje da kasar Sin ta yi amfani da su a watanni 3 na farkon shekarar bana ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 214.57, wanda ya karu da kashi 11.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China