A yayin taron Afrika da Tarayyar Turai da aka kammala a birnin Bruxells, shugaban Zambiya ya kuma zargi kasashen yammacin duniya da gudanar da manufar bita da kulli tare da nahiyar Afrika.
Shugaban mai shekaru 76 a duniya ya fada wa kasashen Turai cewa Afrika bata da kamfanonin dake kera makamai don kara rura wutar yake yake, kana kasashen Turai ne ke bayan wadannan yake yake a nahiyar Afrika domin makaman da ake yaki da su kirar kasashen Turai ne.
A cewarsa yawancin kananan yaran da ake gani cikin yake yake a Afrika suna dauke da makaman da ake kera daga Turai da suka shafi miliyoyin dalar Amurka, tare da kara da cewa in ba haka ba ina wadannan yara matalauta zasu samu kudin sayen wadannan makamai.
Haka kuma mista Sata ya bayyana cewa gwamnatinsa tana maida hankali kan tsarin mulki nagari da ya kasance babban matakin samun cigaba da wadata. (Maman Ada)