Mambobin kwamitin sulhun a cikin sanarwar da suka fitar sun yi suka da kakkausar murya a kan duk hare-haren da neman tashin hankali da ake yi a yankin na Abyei dake karkashin sa idon wucin gadi na sojojin MDD wato UNISFA da wasu masu dauke da makamai ke yi.
Kwamitin mai mambobi 15 daga nan sai suka bukaci gwamnatocin kasashen biyu da cikin gaggawa su binciki wannan harin tare da neman taimako daga sojojin UNISFA inda suka jaddada cewa ya kamata a kame duk masu hannu a cikin wannan danyen aikin don su fuskanci hukunci.
Tun da farko dai a ranar Jumma'an, babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yi suka da kakkausar murya a kan harin da aka kai gidan babban basaraken Abyei, Ngok Dinka. (Fatimah Jibril)