Sanarwar ta ce, kwamintin sulhu na M.D.D. ya yi kakkausar suka da ba a taba ganin irinsa ba ga kungiyar IS, sakamakon kashe dan kasar Sin Fan Jinghui da dan kasar Norway Ole Johan Grimsgaard-Ofstad, kuma wannan aika-aikar da IS ta yi ya nuna rashin imani na kungiyar. Kwamintin sulhu na M.D.D. ya nuna juyayi da janjantawa ga dangogin wadanda suka mutu da gwamnatocin Sin da Norway.
Game da hakan, zaunannen wakilin Sin a M.D.D. Liu Jieyi ya fada wa kafofin yada labaru cewa, kwamintin sulhu na M.D.D. ya mayar da martani bayan da aka hallaka dan kasar Sin, kuma ya yi Ala-wadai da danyen aikin kungiyar 'yan ta'addan, gami da bukatar kasashen duniya da su inganta hadin gwiwa da kasar Sin.
Ya ce duk matakan da aka dauka na nuna cewa mambobin kwamintin sulhu na M.D.D. da ragowar mambobin kasashen M.D.D. sun cimma daidaito game da batun, kana ya bayyana tsayayyiyar anniyar kasashen duniya wajen yaki da laifin ta'addanci. A daya hannun kuma kasar Sin tana adawa da dukkanin nau'in ayyukan ta'addanci, kuma za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasashen duniya, don yaki da duk aika-aikar da ke kawo barazana da wayewar kai ta bil Adama baki daya. (Bako)