Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi ya fadi hakan a ranar Jumma'a, a taron kwamitin tsaron a kan ayyukan wanzar da zaman lafiya, yana mai cewa ya kamata kwamitin ya iya daidaita minzani da manufofin ayyukan wanzar da zaman lafiya bisa tsarin ci gaba da ake da shi sannan a samar da mafita a lokacin da ake bukata.
Ya kuma lura da cewa MDD ya kamata ta inganta kokarin ayyukan wanzar da zaman lafiya sannan ta gaggauta kara yawan jami'an tsaro, ta kara mai da hankali kan kayayyakin jigila da kuma inganta kayayyakin aiki na wanzar da zaman lafiyan.
A gefe daya kuma ya soki mummunan harin ta'addanci da aka kai a ranar Jumma'an a wani otel din kasar Mali, inda yace ayyukan ta'addanci babban makiyin al'umma ne na duniya baki daya yana mai jaddada cewa ya kamata kasashen duniya baki daya su karfafa hadin gwiwwa da kuma hulda a tsakaninsu domin yakar ta'adanci tare.
Mr Liu Jieyi ya kuma ambaci cewa ayyukan zaman lafiya yana da muhimmanci kwarai wajen ci gaba da samar da zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya sannan kuma kasar Sin tana goyon baya sosai ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. (Fatimah Jibril)