Mr Ban wanda ya yi wannan kiran cikin sakon da ya aike a bikin ranar yin hakuri ta duniya ya kuma bayyana cewa, sassan da dama ba sa hakuri da juna, lamarin da ke haifar da karuwar zaman tankiya tsakanin kabilu wadda daga karshe ke haifar da yawan tashe-tashen hankula da karuwar ayyukan ta'addanci.
Mr Ban ya ce, akwai bukatar kasashe da jama'a su kara yin hakuri da juna, kuma za su cimma nasarar hakan ne ta hanyar ilimantar da jama'a, da sanya kowa cikin damammakin da aka samu.
Babban magatakardan ya ce, za a gina al'umma mai zaman lafiya ce ta hanyar mutunta 'yancin bil-adama, wato wurin da kowa ke da dama da 'yanci, ana kuma damawa da kowa ba tare da nuna wani bambanci ba. (Ibrahim)