Wani jami'in tsaro a jihar al-Anbar ya bayyana cewa, sojojin kasar Iraki da sojojin fararen hula sun kai hare-hare har sau uku a birnin Ramadi da ke karkashin ikon kungiyar IS, inda aka yi musayar wuta tsakanin dakarun kungiyar IS da sojojin gwamnatin, lamarin da ya haddasa mutuwar sojojin kasar da mayakan sa-kai a kalla 8, kuma guda 17 suka ji rauni.
A wannan rana, jiragen saman soja na kawancen kasa da kasa dake karkashin jagorancin kasar Amurka sun kai hari ta sama kan birnin Khaldiyah dake da nisan kilomita 80 yamma da birnin Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, harin da ya haddasa mutuwar dakarun kungiyar IS a kalla 15.
Haka zalika jiragen sama masu saukar ungulu na sojojin kasar Iraki sun kai hari kan birnin Fallujah da ke jihar al-Anbar, inda suka hallaka dakarun kungiyar IS 5, da kuma fararen hula 4.
Ban da wannan kuma, wani mutum ya kai harin kunar bakin wake da bam a wata tashar binciken ababan hawa dake yankin Nekheib mai nisan kilomita 400 daga kudancin birnin Ramadi, harin da shi ma ya haddasa mutuwar mayakan 'yan Shi'a 8 da 'yan sanda 2. (Zainab)