Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya nuna jaje ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su. Sannan nan ya nanata goyon baya ga gwamnatin kasar Iraki da kuma jama'ar kasar. Bugu da kari Ban Ki-moon ya yi fatan ganin an gurfanar da wanda ke da hannu a cikin lamarin tun da wuri.
A ranar 17 ga wata ne, aka dasa boma-bomai da ke cikin wata babbar mota a wata kasuwar da ke lardin Diyala na gabashin kasar Iraki, suka fashe a yayin da dimbin mazauna wurin ke sayen kayayyaki don murnar karamin salla. Harin kuwa ya haddasa mutuwa da jikkatar dimbin mutane, baya ga lalata shaguna fiye da goma da motoci da dama.
Tun bayan farkon shekarar 2013, ake cigaba da samun hare-haren ta'addanci da na nuna karfin tuwo a kasar Iraki. Bisa kididdigar da tawagar ba da tallafi ta MDD da ke Iraki ta bayar, an ce, hare-hare da suka faru a shekarar 2014 sun haddasa mutuwar mutane 12,282, yayin da wasu dubu 23 suka jikkata.(Kande Gao)