Rundunar tsaron Nigeriya na farautar 'yan kungiyar ta'addan da suka tsere, sannan suna kuma kokarin dakile duk wani yunkurin wani hari daga kungiyar a sassan yankin arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar sojin kasar a wannan yankin Kanar Sani Usman a cikin sanarwar da ya fitar wa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno ya ce, wuraren da 'yan ya'addan suka kai wa hari kwanan nan shi ma an kara yawan jami'an tsaro, kuma sojojin a shirye suke su shawo kan lamarin a nan gaba.
Kanar Usman ya ce, a makonnin dake tafe za'a tsananta bincike domin tabbatar da an tarwatsa duk wani maboyar kungiyar.
A cewar shi, sojin Nigeriya na kara jaddada aniyar yakar kungiyar ta Boko Haram tare da fatan ganin bayan ta gaba daya.
A don haka ya nemi hadin kan 'yan Nigeria da goyon bayan su tare da fahimtar manufar rundunar tsaron a cikin ayyukan da za su yi.(Fatimah)