in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dakatar da sakonnin wayar salula a Afirka ta Tsakiya don kaucewa barkewar rikici
2014-06-06 15:33:32 cri
Gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya ta sanar da daukar karin matakan tabbatar da tsaro a kasa, ciki hadda dakatar da musayar sakonni ta wayar salula a dukkan sassan kasar tun daga ranar 2 ga watan nan.

Mahukuntan kasar sun kuma ce sai a nan gaba za a bayyana lokacin da za sake ci gaba da aiki da irin wadannan sakwanni.

Yayin da yake bayyana sabuwar dokar ga al'ummar kasar, firaministan Afirka ta tsakiyar Andre Nzapayeke, ya umurni manyan kamfanonin sadarwar dake kasar guda 4, da su tabbatar da kiyaye wannan doka yadda ya kamata.

Rahotanni na cewa kafa wannan doka wani mataki ne na hana dakarun kungiyar Seleka, yin amfani da kafar aika sakwannin wajen rura wutar rikici.

Wannan doka dai ta biyo bayan zargin da aka yi a baya cewa, kungiyar 'yan adawar ta Seleka ta rika gudanar da zanga-zanga tsawon wasu kwanaki a Bangi, kana da rika amfani da musayar sakonni ta wayar salula wajen tunzura jama'a su shiga yajin aiki da tada rikici.

A 'yan watannin da suka gabata dai kungiyar mabiya addinin Kirista ta anti-Balaka, da kungiyar Seleka ta musulmi sun yi ta dauki ba dadi a birnin Bangi, lamarin da ya haddasa salwantar rayukan mutuwa da dama, tare da raunata mutane fiye da dubu 2. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China