Mr Wu ya yi wannan kiran ne yayin da ya ke jawabi a taron kolin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD karo na 66 kan batun 'yan gudun hijirar kasar Afghanistan.
Wu Hailong ya bayyana cewa, a sakamakon yake-yake da rikice-rikice, kasar Afghanistan ta kasance daya daga cikin manyan kasashen da suka fi fama da matsalar 'yan gudun hijira a duniya. Batun 'yan gudun hijira na kasar Afghanistan yana da nasaba da yunkurin sake gina kasar, kana ya yi babban tasiri ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar har ma a yankin baki daya.
Muddin ana bukatar warware matsalar 'yan gudun hijira a kasar, wajibi ne a yi kokarin shimfida zaman lafiya da sake gina kasar da kuma samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar.
Wu ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan ganin an kara zuba jari da kara yin hadin gwiwa da kuma samar da sharadi don warware matsalar 'yan gudun hijira a kasar Afghanistan. (Zainab)