An ji wata babbar kara, sannan wasu hare hare da gurmeti da kuma harbe harben bindigogi suka turmuke shiyyar Qsaba, yankin da ke arewacin filin jiragen saman kasa da kasa na Kaboul, da misalin karfe goma ne na dare, agogon wurin, in ji Wasim Hakimi, wani mazauni wurin da lamarin ya faru a gaban idonsa.
Ga yadda harin ya faru ana kyautata zaton cewa hari ne da mayakan Taliban suka shirya da wata motar da shake da bama bamai a kan ginin, sannan suka yi ta barin wuta, in ji Wasim Hakimi.
Wadannan hare hare sun kasance na uku da aka kai a birnin Kaboul a cikin sa'o'i 24 na baya bayan nan.
A ranar Jumma'a da yamma, dalibai 26 aka kashe yayin da wasu 27 jikkata a wani harin kunar bakin wake kan ginin makarantar horar da 'yan sanda, dake yammacin birnin Kaboul, wanda kungiyar Taliban ta dauki alhakin kaiwa.
Haka zalika a ranar, fararen hula 15 aka kashe, a yayin da wasu 240 suka jikkata a wani harin mota a kudu maso gabashin Kaboul. (Maman Ada)