in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da kai mummunan hari ta jiragen sama kan asibiti a Afghanistan
2015-10-04 14:09:40 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki Moon, ya yi Allah wadai da kai wani kazamin hari ta jiaragen sama wanda ya hallaka ma'aikatan lafiya da fararen hula a wani asibiti dake arewacin Afghanistan, sannan ya yi kira da a gudanar da bincike domin gano wadanda suka kaddamar da harin domin hukunta su.

A safiyar ranar asabar ne, aka bada rahoton wasu mayakan Amurka sun kai hari kan asibitin Medecins Sans Frontieres dake birnin Kunduz a arewacin lardin Kunduz kuma harin ya hallaka mutane 19 sannan wasu 37 sun samu raunuka.

Tun da farko shugaban kasar ta Afghaniostan Mohammad Ashraf Ghani, ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin wanda ya yi sanadiyyar kashe rayuka da kuma raunata ma'aikatan lafiya da fararen hula a kasar.

Rahotannin sun ce, cikin wadanda harin ya rutsa da su har da yara kanana su 3.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China