Wakilai daga kasashe 17 da MDD da kungiyar EU masu halartar taron sun zartas da wani shiri a wannan rana, inda suka nuna goyon baya ga neman tsagaita bude wuta a dukkan kasar Sham bisa jagorancin MDD tare da sake aiwatar da harkokin siyasa a kasar. Kana a karkashin sa ido daga MDD, za a zabi sabon shugaban kasar ta hanyar yin zabe cikin 'yanci a kasar.
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun Sham Staffan de Mistura da kuma ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov sun gudanar da taron manema labaru na hadin gwiwa bayan taron.
Mr Kerry ya bayyana cewa, wannan ne mafarin sabon yunkurin harkokin diplomsiyya. Ya ce, yayin da ake ingiza yunkurin samar da wani yanayi na wucin gadi a kasar, za a fitar da sabon kundin tsarin mulkin kasar, kana za a gudanar da zaben kasar bisa sa ido daga kasa da kasa, kuma sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu adawa za su tsagaita bude wuta.
Hakazalika kuma, Mr Kerry da Mr Lavrov sun bayyana cewa, ana ci gaba da samun bambancin ra'ayi kan batun shugaban kasar Sham Bashar Hafez al-Assad, amma wannan bai kamata ya jawo cikas ga cimma shirin warware batun kasar ta hanyar siyasa ba. Mr Lavrov ya kara da cewa, makomar shugaba Bashar tana hannun jama'ar kasar Sham, kuma kasar Rasha ta yi imani da cewa, ya zama dole a warware batun yayin da ake ingiza yunkurin siyasa a kasar. (Zainab)