in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Congo ya yi kiran shirya zaben raba gardama kan batun canja kundin tsarin mulki
2015-09-24 13:12:26 cri
Shugaban kasar Congo, Denis Sassou N'Guesso, ya yi kira a ranar Talata da yamma a birnin Brazzaville, kan batun shirya wani zaben raba gardama, domin amincewa da wani sabon kundin tsarin mulki. "Na dauki niyyar baiwa al'ummar kasa zabi kai tsaye domin su bayyana ra'ayinsu kan shirin dokar dake bayyana muhimman sharudan jamhuriya da tsaida sabbin tsare tsare na shiryawa da sabbin matakan dake tafiyar da aikin gwamnati, in ji shugaba Sassou N'Guesso a cikin wani jawabi na rediyo da talabajin. Bai tsaida ranar da za a shirya wannan zaben raba gardama ba. Amma duk da haka ya bayyana cewa, za a kafa wani kwamitin da aka dora wa nauyin tsara kundin tsarin mulki da kira zaben raba gardaman nan da lokaci kalilan. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China