in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid da Atletico Madrid sun rage tazara tsakanin su da Barcelona
2015-12-07 11:18:23 cri
A ci gaba da buga gasar La Liga ta kasar Sifaniya, Real Madrid da Atletico Madrid sun kara rage tazarar dake tsakanin su da Barcelona wadda ke samar teburin na La Liga, bayan da suka samu nasara a wassanni su na karshen mako. Yayin da a daya bangaren Barcelona ta buga kunnen doki 1 da 1 da kungiyar Valencia.

Yayin wasan da Real Madrid ta buga da Getafe, Madrid din ta samu nasara kan Getafe da ci 4 da 1. A wasan, Karim Benzema ya ci kwallaye biyu ga Madrid kafin tafiya hutun rabin lokaci, yayin da kuma Gareth Bale da Cristiano Ronaldo suka kara kwallaye dai-daya.

Kafin hakan 'yan kallo sun rika yiwa kocin kungiyar Rafael Benitez, da shugaban ta Florentino Perez ihu, sakamakon fidda kungiyar daga jerin kulaflikan da za su buga gasar King's Cup.

A nata bangare Getafe ta samu damar zura kwallo daya a ragar Real Madrid, ta hannun dan wasan ta Alexis, mintuna 20 kafin tashi daga wasan.

Shi ma kulaf din Atletico Madrid ya samu nasara ne kan Granada da ci 2 da nema ta hannun Diego Godin da Antoine Griezmann.

Wadannan sakamako biyu tamkar matsin lamba ne ga Barcelona dake matsayi daya a teburin gasar da maki 34. Sai kuma Atletico Madrid dake matsayi na biyu da maki 32, yayin da Real Madrid ke biye da maki 30.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China