in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Arsenal ta lallasa Sunderland da ci 3 da1 a gasar Premier
2015-12-07 11:14:48 cri
Arsenal ta samu nasarar zara kwallaye 3 a ragar Sunderland a wasan da aka buga ranar Asabar din da ta gabata, yayin da Sunderland ta zara kwallo daya tal a gasar, lamarin da ya sa ta sha kaye a wasan ta zagaye na 3.

Dan wasan gaba na kulub din na kasar Faransa Olivier Giroud, ya yi nasarar zara kwallon ne a karo na biyu na lokacin fara wasan, kuma zara kwallon tasa ne ya baiwa kulub din nasarar zuwa zagaye na biyu na gasar ta Premier.

Joel Campbell, shine ya zara kwallo ta farko mintuna 33 da fara wasan, yayin da Giroud ya bi masa baya. Aaron Ramsey shi ne ya zara kwallo ta 3, lamarin da ya tabbatarwa kulub din su nasara a gasar.

Yanzu haka Arsenal tana da maki biyu, kuma tana sama da Leicester wanda da farko take gaban ta, yayin da Sunderland ke da maki biyu ta fita daga sahun koma baya.

Idan har Arsenal ta samu nasara a wasan ta na mako mai zuwa, zai bata damar kaiwa ga zagayen karshe na gasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China