in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FIFA ta yi watsi da bukatar Blatter, da Platini na kalubalantar ta
2015-11-19 15:30:30 cri
Kwamitin sa ido kan daukaka kara na hukumar FIFA a ranar Larabar nan, ya yi fatali da korafin da tsohon shugaban hukumar Sepp Blatter da takwaransa Michel Platini suka gabatar na dakatar da su daga al'amurran hukumar na tsawon kwanakin 90, sakamakon zarge zarge da ake yi musu na almundanar kudade.

An dakatar da jami'an biyu ne tun a ranar 7 ga watan Oktoba, inda kwamitin da'a na hukumar ta FIFA ya ce yana bukatar gudanar da cikakken bincike kan al'amarin, domin bankado zargin yin sama da fadi da kudaden da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 2, wanda ake zargin Blatter ya biya kudaden ga Platini ba bisa ka'ida ba a shekarar 2011 a matsayin kudaden albashi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China