in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiya ta kama wasu jiragen ruwan Rasha a cikin ruwan tekun Black
2015-12-07 10:46:55 cri
Kasar Turkiya ta kama wasu jiragen ruwan Rasha hudu kusa da tashar ruwan Samsun, dake arewacin ruwan tekun Black, a cikin wani matakin mayar da martani ga kasar Rasha dake take tsangomar jiragen ruwan Turkiya, in ji kamfanin dillancin labaran Turkiya Ihlas a ranar Lahadi. Hukumomin Turkiya sun kama jiragen ruwan Rasha hudu dalilin rashin takardun da ake bukata, uku daga cikinsu an bar su sun wuce bayan sun ciki takardun, yayin da jirgin ruwan na hudu ake cigaba da tsare shi a tashar ruwan, in ji hukumomin tashar jiragen ruwan.

A makon da ya gabata, Rasha ta hana jiragen Turkiya biyar shiga tashar jiragen ruwanta, ta Novorossik. Dangantaka dai tsakanin Ankara da Moscow ta kara tsami tun bayan da Turkiya ta harbo wani jirgin yakin Rasha a ranar 24 ga watan Nuwamba, tare da bayyana cewa jirgin yakin na Rasha ya ratsa sararin saman ta. Lamarin da Moscow ta karyata tare da jaddada cewa jirgin yakinta na cikin sararin saman Syria a lokacin da Turkiya ta harbo shi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China