A jiya ne da misalin karfe 8 na dare agogon kasar Afirka ta kudu, shugaba Xi da uwar gidansa sun halarci bikin tare da takwaransa na Afirka ta Kudu, Jacob Zuma da uwar gidansa, da kuma sauran shugabannin da suka halarci taron kolin FOCAC na Johannesburg inda 'yan kallo kimanin dubu daya da suka halarci bikin suka mike tsaye suka tafa. Wannan bikin kide kide da wake wake mai taken "Lokacin Sin da nahiyar Afirka" ya samu halartar mawaka da makida na Sin da na kasashen Afirka kimanin 200.(Fatima)