Ministar harkokin wajen kasar Ghana Hanna Serwaa Tetteh, ta ce kasashen Afrika sun shirya tsab domin halartar babban taron dandalin tattaunawar hadin kan kasashen Sin da Afrika wato FOCAC, wanda ake sa ran gudanarwa a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu a ranakun 4 zuwa 5 ga watan nan na Disamba.
Ta ce, kasashen Afrika za su shiga a dama da su a taron, domin sauraron muhimman bayanai daga takwaransu kasar Sin, da kuma tattauna muhimman batutuwan da suka shafi hadin kan dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.
A yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua Tetteh, ta ce yana da muhimmanci a yi nazari kan muhimman hanyoyin da za su kara tabbatar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu a lokacin gudanar da taron na FOCAC, kasancewar dukkannin bangarorin na da muradin dorewar wannan dangantaka.
Taron FOCAC na bana shi ne karo na 15, kuma shi ne karon farko da za'a gudanar a nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)