in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron masana shari'a na FOCAC ya bukaci a lalibo hanyoyin kara hadin kan Sin da Afrika
2015-11-27 10:32:58 cri

Taron tattaunawa kan batutuwan shari'a na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika FOCAC a ranar Alhamis din nan a Johannesburg, wanda ya samu halartar wakilai daga kasashen Afrika da kasar Sin ya bukaci da a lalibo hanyoyin da za su taimaka wajen samar da karin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Da yake jawabi a yayin taron, babban daraktan hulda da kasashen waje na kasar Sin a fannin shari'a Guo Zhaomin ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi musayar ilmi da kwarewa da kasashen African.

Guo ya kara da cewa, dama dai kasar Sin ta rabbata hannu kan kudurin dokoki na New York, wadanda suka dace da daftarin dokoki na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya. Kuma a shirye suke su goyi bayan duk wani tsari da zai kara dankon zumunci a huldar dake tsakanin Sin da Afrika ba tare da yiwa dokokin duniya karan tsaye ba. Wasu daga cikin dokokin ba su yiwa kasashe masu tasowa adalci ba. Dole ne a kyautata tsarin dokokin, ta yadda za su dace da muradun kasashen masu tasowa.

Ya ce, taron shugabannin dandalin FOCAC dake tafe, tamkar dama ce da za ta samar da wasu sabbin damammaki.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China