Dandalin hadin gwiwwa tsakanin Sin da nahiyar Afrika wato FOCAC dake tafe babbar shaida ce a kan manufar kasar Sin ta son yin hadin gwiwa da zai kawo moriyar juna gaba daya tsakaninta da kasashen Afrika, in ji wani masani kan harkokin ci gaba.
Taron da za'a yi shi a tsakanin ranakun 4 zuwa 5 ga watan nan na Disamba a Johannesburg, zai zama taron shugabannin FOCAC karo na biyu da za'a yi shi a cikin shekaru 15, kuma na farko a nahiyar Afrika.
Farfesa Francis Chigunta ya yaba wa Sin game da yadda za ta aiwatar da taron wannan karon a nahiyar Afrika wanda ya nuna muhimmancin da ta dora a kan huldar dake tsakaninta da nahiyar.
Masanin wanda babban malami ne a makarantar ayyukan ci gaba a jami'ar Zambiya ya kara bayanin cewa, yin wannan taron a nahiyar Afrika har ila yau wani abu ne da Sin ke son nuna wa duniya cewa, ba ta da wani manufa ta mulkin mallaka, kuma tana da aniyar ganin an samar da kayayyakin ci gaba a kasashen Afrika.(Fatimah)