in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Afrika suna sa ran sosai game da taron kolin FOCAC
2015-11-30 13:56:21 cri
Daga ranar 4 zuwa ranar 5 ga watan Disamba, za a gudanar da taron koli tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a kasar Afrika ta Kudu, taron da shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Jocab Zuma na Afrika ta Kudu za su jagoranta tare a birnin Johannesburg. Shugabanni da kusoshin gwamnatoci, da ministoci na kasashen Afrika, suna sa ran cimma nasarori game da taron, sun kuma jinjinawa goyon baya da Sin ta samar ga ci gaban nahiyar.

Mataimakin shugaban tarayyar Nijeriya Oluyemi Osinbajo ya ce, Nijeriya ta dora muhimmanci sosai game da alakarta da kasar Sin, kuma ta mayar da Sin a matsayin wata babbar kawar hadin gwiwa, kana ta yaba wa goyon baya da Sin ke bayarwa game da raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Nijeriya, kazalika ya yi fatan Nijeriya za ta yi koyi daga fasahohin Sin ta fuskar ci gaba. Ya ce, yayin da Nijeriya ke shiga sabon mataki na raya kasa, tana fuskantar babbar damar samun bunkasuwa, tana kuma maraba da Sin, wajen kara zuba jari a fannin samar da muhimman ababen more rayuwa, don sa kaimi ga raya zirga-zirga da samar da wutar lantarki a Nijeriya, don kawo moriya ga jama'ar kasashen biyu.

A daya bangaren kuma, a matsayinta na kasar da za ta shirya taron, ministar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu Nkoana-Mashabane, ta ce, bisa ka'idar inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, Sin da Afrika sun kasance cikin daidaito, da haifar da moriya ga bangarorin biyu, da dora muhimmanci game da raya tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasashen Afrika, da dunkulewar tattalin arzikin kasashen Afrika baki daya, musamman ma wajen raya muhimman ababen more rayuwa da soke basussukan da aka ci, da raya masana'antu. Ministar ta ce, kasar Afrika ta Kudu tana da imani cewa, za a shirya taron cikin nasara, don kyautata dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, da kawo moriyar juna, da samun ci gaba, don kyautata zaman rayuwar al'ummar Afrika da na kasar Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China