A jiya da yamma ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake ganawa da firaministan kasar Birtaniya David Cameron a fadarsa ta Chequers.
Firaminista David Cameron ya marabci shugaba Xi a lokacin da ya fito daga motar da ya ke ciki. Daga baya, suka tafi filin ciyayi domin dasa wani nau'in iccen da ke alamanta dankon zumunci a tsakanin kasashen Sin da Birtaniya.
David Cameron ya bayyana farin cikinsa da ziyarar aiki da Xi Jinping ya kawo kasar ta Birtaniya.
A jawabinsa Mr. Xi ya bayyana cewa, ya samu nasara a ziyarar aikin da ya kawo,kana ya samu sakamako da dama, ya kuma yi imani sosai ga kyakkyawan yanayin hulda a tsakanin kasashen biyu.
Bayan ganawar, shugabannin biyu sun yi tattaki zuwa mashayar dake wajen gari kamar yadda aka saba yi bisa al'adu, inda suka ci soyayyen kifi da soyayyen dankali kana suka sha giya, daga bisani kuma suka zanta da mazauna garin.(Lami)