A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wani muhimmin jawabi mai taken "bude kofa da yin hakuri da juna don neman samun bunkasuwa cikin lumana" a cibiyar hada-hadar kudi ta birnin London, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da Birtaniya su kafa wani sabon tsari na hulda tsakanin kasashen biyu bisa hangen nesa da ka'idojin bude kofa, da yin hakuri da juna, da hadin gwiwa, gami da cin moriyar juna, ta yadda za su kara ba da gundummawa wajen neman samun bunkasuwa cikin lumana.
Game da batun ci gaban kasar Sin kuwa, Shugaba Xi ya ce da farko jama'ar kasar Sin na bin hanyar da ta fi dacewa da tsarin tarihinsu. Kasar Sin ta samu sakamako mai kyau ta hanyar bin tsarin gurguzu a cikin shekaru gomai kamar yadda kasashe masu sukuni suka samu a cikin shekaru fiye da dari daya, hakan ya shaida cewa, jama'ar Sin suna kan hanya mafi dacewa.
Na biyu, kasar Sin ita ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya. Jama'ar kasar suna kara yin kokari don ci gaba da kyautata yanayin zamantakewar rayuwarsu.
Na uku, jama'ar Sin suna bukatar samun bunkasuwa cikin lumana a duniya. Kuma kasar Sin ba za ta hana ci gaban sauran kasashen duniya ba, sai dai ma ta haifar da cin moriyar juna a tsakanin kasashen duniya.(Lami)