Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Lu Kang ya sanar a yau Laraba cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Faransa Francois Hollande da shugaban taron sauyawar yanayi na duniya Laurent Fabius suka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron sauyawar yanayi na duniya a birnin Paris na kasar Faransa daga ranar 29 zuwa ranar 30 ga wata.
Ban da haka kuma, bisa gayyatar da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi masa, Xi zai kai ziyarar aiki a kasarsa daga ranar 1 zuwa ranar 2 ga watan Disamba.
Bugu da kari, bisa gayyatar da shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya yi masa, shugaba Xi zai kai ziyarar aiki a kasar daga ranar 2 zuwa ranar 5 ga watan Disamba, kuma zai jagoranci taron koli na dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika a birnin Johnnesburg.(Lami)